Dr. Muhammad Ali Pate Janye Daga Shugabancin Vaccine Alliance

Dr. Muhammad Ali Pate-Nigeria's Former Minister of State for Health

Sabon shugaban hukumar samar da rigakafi ta Gavi Vaccine Alliance, Dan Najeriya Dr. Muhammad Ali Pate, ya ajiye mukaminsa na shugabancin hukumar mai zaman kan ta domin ba da gudunmawar shi wajen gina kasarsa.

A ranar uku ga watan Agustan bana ne ya kamata Dr. Muhammad Ali Pate ya kama aiki a matsayin shugaban hukumar samar da alluran rigakafi ta duniya wato Global Vaccine Alliance .

Hukumar ta sanar a watan Fabrairu cewa Pate zai gaji tsohon shugabanta dan kasar Amurka kuma kwararre a fannin binciken cuttutuka Seth Berkley wanda ya rike da mukamin tun shekara ta 2011.

A wata sanarwa a jiya Litinin, hukumar ta Gavi Global Vaccine Alliance ta ce, "Dr. Ali Pate wanda ya rike manyan mukamai a bangaren lafiya a Najeriya ya ajiye aikin shi bayan da aka bukaci kwarewarsa a kasarsa ta Najeriya."

Matakin na Pate na da nasaba da bukatarsa a sabuwar gwamnatin Tinubu wadda yanzu haka ta ke kokarin nade-naden sabbin mukamai tun bayan da ya kama aiki a matsayin shugaban kasar Najeriya.

Dr. Muhammad Ali Pate-Nigeria's former minister of state for health

Dr. Ali Pate kwararren likita ne a fannin ilmin cuttutuka masu yaduwa kuma farfesa a jami’ar Havard da ke Amurka wanda a baya ya rike mukamin shugaban hukumar lafiya a matakin farko na Najeriya NPHCDA da kuma karamin ministan lafiya inda ya taka mahimmiyar rawa a fannin tsarin aikin lafiya.

Yanzu dai babban jami’in gudanarwa a Gavi David Marlow, zai ja ragamar hukumar a matsayin rikon kwarya kafin kungiyar ta samo wani wanda za ta nada a sabon shugabanci.

Gavi Vaccine Alliance hukuma ce mai zaman kan ta wanda aka kafa a shekara ta 2000 domin samar wa kasashe masu tasowa alluran rigakafi daban daban musamman ma kasashe masu kananan karfi 73.

Gavi ce take kan gaba a batun rigakafin Covax tare da hukumar lafiya ta duniya da kuma gammayar kungiyoyi masu rajin tunkarar cututukan annoba.

Ya zuwa yanzu dai kungiyar ta samar da rigakafin korona kusan biliyan 1.9 a kasashe 146.