Doug Fibbioli ya nuna damuwarsa akan makomar tattalin arzikin karkara, yayinda gine-gine ke cigaba da maida gonaki da filayen kiwo birane. Wani mai masana’antar hada ruwan enabi a jihar Virginia dake Amurka, ya yanke shawarar zama mafita a wannan matsalar, sai ya bude wata makaranta da ake kira The New AG School, makasudin makarantar shine gina manoma masu tasowa.
Kasancewa manomi aiki ne mai wahala, amma Fabbioli ya ce idan matasa sun san farin cikin da alherin dake tattare da noma, za su so hakan. Amma idan har suna so su sami nasara, to da bukatar su sami karin ilimi na musamman.
Abinda Fabbioli yake fatan koyawa kenan a sabuwar makarantarsa. Burinsa shine biyan babbar bukatar manoma, amma kuma don ya horar da manoma masu tasowa, wadanda zasu zama abin koyi, su kuma koyawa wasu sabbin manoman yadda zasu yi sana’ar.
Makarantar wadda kyauta ce na koyawa dalibanta abubuwa daki-da-daki da kuma yadda za a yi su.