Shugaban Philippine, Rodrigo Duterte ya ce shugaba mai jiran-gado Donald Trump ya kira shi ta wayar talho, inda ya yi mai fatan alheri dangane da yakin da ya ke yi da masu safarar miyagun kwayoyi, yakin da ya halaka mutane sama da dubu hudu tun daga watan Yuli.
WASHINGTON D.C. —
A cewar Duterte, Trump ya yaba da yadda ya ke yakin da masu safarar muggan kwayoyi a matsayin Philippines na kasa mai cin gashin kanta.
A dai farkon shekarar nan ne Duterte ya lashe zaben kasar ta Philippines, inda a lokacin yakin neman zabensa ya yi alkawarin kawar da masu safara da amfani da muggan kwayoyi.
Tun bayan da ya karbi ragamar mulkin kasar ta Philippine, Duterte ya ke jefawa hukumomin Washington bakaken magana, lamarin da ake ganin zai iya kawo cikas ga huldar diplomasiyyar kasashen biyu.