Donald Trump Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Goyon Bayan Masu Zanga-zanga A Hong Kong

Shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannun amincewa da kudurorin doka 2 da ke goyon bayan masu zanga-zangar tabbatar da dimokaradiyya a Hong Kong, duk kuwa da kawancen kasuwanci da ke tsakaninsu da Beijing.

Majalisar dattawa da ta wakilai duk sun amince da kudurorin da kusan murya daya a makon da ya gabata.

Daya dokar ta yi tanadin cewa ma’aikatar harakokin wajen Amurka ta tabbatar kowace shekara, China tana baiwa Hong Kong cikakken ‘yancin cin gashin kai, domin ba ta damar shata yanayin kasuwanci da ya dace da ita. Dokar ta yi baranar kakaba takunkumi ga jami’an China da suka yi kunnen kashi.

Doka ta 2 kuma ta yi haramcin fitar da hayaki mai sa hawaye da barkonon tsohuwa da albarusan roba, da kuma kananan makamai zuwa ga ‘yan sandan Hong Kong.

Beijing ta yi barazanar daukar matakan ramuwa muddin Trump ya sanya hannu ga dokokin, tana mai cewa Amurka na yin shisshigi a lamurran cikin gida na kasar ta China.

China ta yi gargadin cewa sakamakon haka kuma ba zai haifar da da mai ido ba.

To sai dai kuma da yake bayani a kafar talabijin ta Fox News, Trump ya bayyana shugaban China Xi Jinping a matsayin abokinsa, kuma mutumin kirki.

Ya kara da cewa ya rattaba hannu a kan dokokin cikin girmamawa ga shugaban na China Xi Jinping, kuma suna da manufar ganin cewa shugabanni da wakilan jama’a a China da Hong Kong, za su sasanta tankiyar su cikin ruwan sanyi, wanda zai kai ga samun dauwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali.