Yayinda ya saura kwana uku a rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban Amurka, Muryar Amurka ta zagaya ta ji ra'ayoyin wasu 'yan Kamaru inda wasu suke ganin babu abun da zai yiwa kasashen Afirka
WASHINGTON DC —
Wanda ya fara magana yace hawansa kan kujerar mulkin Amurka ba zai tsinana masu komi ba saboda ko Obama dake da jini Afrika basu ga abin da ya yiwa Afirka ba.
Wani yace gaskiya za'a rantsar da Donald Trump amma a nahiyar Afirka menene muradun mu, inji shi. A cewarsa da rantsar dashi da rashin rantsar dashi duk daya ne gareshi domin matsalar "kasarsu ce".Yace su yi can tsakaninsu domin "mu ma mutanen Afirka muna da matsalolinmu" a cewarsa.
To sai dai wani yana ganin Donald Trump zai sake wasu abubuwa da dama musamman a nahiyar Afirka. Yace ya zo ne ya kawo gyara. Yace ko shakka babu Trump nada tashi siyasar da kuma akida da ya sa gabansa.
Ga rahoton Garba Awal da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5