Shugaban kungiyar babban dan siyasar arewa Tanko Yakasai ya bayyana haka a taron da ya jagorantar na kungiyar don bitar zaben da ya gudana.
Kungiyar da ke da ‘yan boko, malaman jami’a da masu sarautar gargajiya na arewa ta kasance kan gaba cikin masu karfafa mulkin karba-karba tsakanin kudanci da arewacin.
Alhaji Tanko Yakasai ya ce tarihin siyasar arewa kan dauki duk ‘yan kasa a matsayin masu ‘yanci ta hanyar kauce wa duk wani tsari na nuna wariya musamman kan kabilanci.
Alamun zaben da a ka gudanar ya samu karbuwa a arewa a ta bakin Alhaji Yakasai shi ne yanda jama’a su ka karbi sakamakon cikin lumana.
Shi ma jami’in hulda da jama’a na kungiyar Farfesa Ibrahim A Madugu na jami’ar Ahmadu Bello, ya ce su na da kwarin gwiwar yankin arewa zai ci gajiyar mulkin na karba-karba.
Hakanan kungiyar ta bukaci ‘yan arewa su fito ranar Asabar din nan don kada kuri’arsu ga ‘yan takarar gwamna da ‘yan majalisar jiha da su ka kwanta mu su a rai don samun cigaba daga tushe.
In za a tuna takwarar kungiyar zauren dattawan arewa karkashin farfesa Ango Abdullahi bai dau matsaya ta kai tsaye kan wanda za a zaba ba, inda ya bar kofa bude na masu zabe su dubi abun da ya fi zama a’ala.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5