DOMIN IYALI: Nazari Kan Nawaitawa Kananan Yara -Kashi Na Biyu, Satumba, 29, 2022

Alheri Grace Abdu

Makon da ya gabata, shirin Domin Iyali fara haska fitila kan wata matsala da ake dangantawa da bautar da kananan yara a Jamhuriya Nijar, inda kamar kasashen nahiyar Afrika da dama, ake sa kananan yara ayyukan da suka fi karfin shekarunsu, da idan haka ta faru a kasashen da suka ci gaba, zai kai ga yiwa iyayen hukumci mai tsanani a wadansu lokutan ma har hukuma ta kwace ‘ya’yan domin kare hakkokinsu.

Yau ma muna tare da Bachar Maman shugaban gamayyar kungiyoyin fararen Reseau Esperance , da dan jarida kuma babban editan jaridar La Roue de l’Histoir Ibrahim Moussa.

A makon da ya gabata Bashar Mammane ya fara bayyana dalilai uku da ya ce su ne sanadin bautar da kananan yara lokaci ya kwace mana, inda kuma shirin ya dora ke nan yau a tattaunawar da wakilinmu Souley Mummuni Barma ya jagoranta.

Saurari cikakken shirin:

Your browser doesn’t support HTML5

DOMIN IYALI: Nazari Kan Nawaitawa Kananan Yara -Kashi Na Biyu