Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Nazari Kan Nawaitawa Kananan Yara -Kashi Na Daya, Satumba, 22, 2022


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Duk da kiraye kirayen da gwamnatoci da kungiyoyi ke yi domin ganar da al’umma illolin dake tattare da dabi’ar bautar da yara kanana ko kuma sa su ayyukan da su ka fi karfin shekarunsu a kasashe masu tasowa, bincike na nuni da cewa, har yanzu ba ta canza zane ba. Lamarin da ake dangantawa da tarin dalilai masu nasaba da jahlici ko al’adu da matsalolin tattalin arziki.

Jamhuriyar Nijer na daga cikin kasashen da ake fama da wannan matsala da saka yara aikin da ya fi karfinsu inda a wasu yankunan a ke tura yara kanana su yi aiki domin samar wa mahaifansu kudin kashewa ko kuma na daukan dawainiyar iyali. Lamarin da ya sa wasu iyayen ke bada ‘ya'yansu haya zuwa kasashen waje da nufin neman kudi.

Haka kuma ake ci gaba da samun kawarar kananan ‘yan matan karkara zuwa manyan biranen kasar domin su yi aikatau ko kuma wasu ayyukan da ba su dace da masu kananan shekaru ba.

Wannan ya sa shirin DOMIN IYALI ya shirya tantaunawar musamman da masu ruwa da tsaki akan maganar kare hakkokin yara da nufin neman hanyar shawo kan matsalar.

Bakin namu, Bachar Maman shugaban gamayyar kungiyoyin fararen hula ta Reseau Esperance, da dan jarida kuma babban editan jaridar La Roue de l’Histoire Ibrahim Moussa.

Saurari kashin farko na tattaunawar da wakilinmu Souley Mummuni Barma ya jagoranta:

DOMIN IYALI: Nazari Kan Nawaitawa Kananan Yara-Kashi Na Daya
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:22 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG