DOMIN IYALI: Nazari Kan Matsalar Yawan Mace-Macen Aure a Jamhuriyar Nijar-Kashi Na Biyu, Maris, 03, 2022

Alheri Grace Abdu

A yau shirin Domin Iyali ya koma kan nazarin da mu ka fara dangane da batun karuwar mace macen aure da ake fuskanta a dukan jihohin Jamhuriya Nijar inda bayanai ke nuni da cewa, an sami mutuwar aure sama da 3000 a shekarar da ta gabata a birnin yamai kawai, yayinda a jihar Agadas rahotanni ke nuni da cewa, a kowacce rana akan sami karafe korafen neman kashe aure a kalla shida, a kuma raba a kalla uku daga ciki.

Rahoton ya kuma nuna cewa, shekara ta 2021 ce shekarar da aka fi samun yawan mace macen aure a Jamhuriyar Nijar baki daya

Bakin da muka gayyata domin neman sanin masababin wannan lamarin da kuma hanyar magance ta su ne, Hajiya Halima Sarmay dattijiya kuma daya daga cikin shugabannin kungiyar kare hakkin mata da kananan yara, da Malan sani Sabiou Souleyman shugaban kungiyar addinn Islama ta Aisef, da kuma Falmata Moctar Taya shugaban kungiyar matasa.

Saurari tattaunawar da Souley Moumouni Barma ya jagoranta.

Your browser doesn’t support HTML5

DOMIN IYALI: Nazari Kan Matsalar Yawan Mace-Macen Aure a Jamhuriya Nijar-Kashi Na Biyu -10:00"