Batu na karshe da muka yi mukala a kai a shekarar da ta gabata shine matsalar mace macen aure a Arewacin Najeriya, muka kuma gayyaci kwararru domin neman hanyar shawo kan wannan matsalar.
A bana, shirin zai fara tashi a Jamhuriyar Nijar inda wani rahoton kungiyar addinin Islama ta AIN mai kula da shiga tsakanin ma’aurata ya nuna cewa, an fuskanci mutuwar aure sama da 3,000 a shekarar da ta gabata a birnin Yamai kawai, lamarin dake kara nuna yadda wannan matsala ke ta’azzara a kowace shekara duk da fadakarwa da jan hankulan da shugabanin addinai ke yiwa jama’a akan mahimmancin igiyar aure.
Kafin hada kan masu ruwa da tsaki domin neman sanin masababin wannan lamarin da kuma hanyar maganceta, wakilinmu a birnin Yamai Souley Moumouni Barma ya yi nazarin lamarin.
Saurari rahoto na musamman da ya hada mana: