DOMIN IYALI: Nazari Kan Koma Bayan Ilimi A Kasar Ghana-Kashi Na Biyu-Nuwamba, 24, 2022

Alheri Grace Abdu

Idan kuna biye da mu, shirin Domin Iyali ya gayyaci masu ruwa da tsaki domin nazarin matakan shawo kan koma bayan harkokin ilimi a arewacin kasar Ghana, daya daga cikin kasashen yammacin Afrika da binciken Babban Bankin Duniya ya nuna ana samun koma baya a fannin ilimin 'ya'ya mata.

Bakin da muka gayyata domin bada gudummuwa ga yunkurin neman mafita sun hada da Abdallah Tobodu: Kodinetan sashen ilmin addinin Musulunci na hukumar ilimi ta Ghana, da Gimbiya Ummul Khair Jafar: ‘yar jarida, da Samira Yahaya AbdurRahman: Babbar jami’a a hukumar wayar da kan al’umma ta kasa (NCCE). Issah Mairago Gibril Abbas: Mai fashin baki a kan al’amuran yau da kullum .

A shirin na yau, Gimbiya Ummul ta fara da bayyana faidar ilimantar da ‘ya’ya mata a ci gaban tattaunawar da wakilinmu a birnin Acrra Idris Abdullah Bako ya jagoranta.

Saurari cikakken shirin cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

DOMIN IYALI: Nazari Kan Koma Bayan Ilimi A Kasar Ghana-Kashi Na Biyu