Washington, dc —
Kamar yadda muka alkawarta, shirin Domin Iyali ya gayyaci masu ruwa da tsaki domin nazarin matakan shawo kan koma bayan harkokin ilimi a arewacin kasar Ghana, daya daga cikin kasashen yammacin Afrika da binciken Babban Bankin Duniya ya nuna hannun agogo na komawa da baya a fannin ilimi.
Bakin da muka gayyata sun hada da Malam Abdallah Tobodu, Koodinetan sashen ilmin addinin Musulunci na hukumar ilimi ta Ghana, da Gimbiya Ummul Khair Jafar ‘yar jarida kuma uwa, da Samira Yahaya AbdurRahman: Babbar jami’a a hukumar wayar da kan al’umma ta kasa (NCCE), da Issah Mairago Gibril Abbas mai fashin baki a kan al’amuran yau da kullum.
Saurari cikakken shirin cikin sauti: