Yau shirin Domin Iyali ya tattauna kan batun sace ‘yammatan Chibok da aka cika shekaru takwas cif yau, da bayanai ke nuni da cewa, har yanzu ba a san yanayin da dari da goma daga cikin dalibai 276 da aka sace su ke ciki ba.
Wakiliyar Sashen Hausa Madina Dauda ta tattauna da shugaban ‘yan asalin Chibok mazauna birnin tarayya Abuja Nkeki Mutah, da Madam Martha Bitrus Dalu ita ma ‘yar asalin Chibok wadda kuma ta rubuta littafi kan sace ‘yan matan.
Saurari kashin farko na tattaunawar:
Your browser doesn’t support HTML5