Wakilin Sashen Hausa Mahmoud Ibrahim Kwari ya tambayi Mallam Kabiru Dakata abinda yasa duk da jami’an da ake dasu a bangarori da ma’aikatu dabam dabam, da sunan wakiltar iyali, ake ci gaba da samun korafe korafe.
Da yake maida martini, kwamred Dakata yace, ba Magana ce ta wanda suke yi masu wakilci basu yin abinda ya kamata ba, Magana ce ta suma matan a matsa masu su shigo a dama da su, domin idan basu da wakilci a teburin da za a zauna a yanke hukumcin da zai shafe su, kuma ya kasance babu su, babu yadda za a yanke hukumcin da zai gamshe su.
Kabiru Dakata yayi misali da jihar Kano inda ake da ‘yan majalisun jiha guda arba’in babu mace, ko daya, da shugabannin kananan hukumomi fiye da arba’in, babu mace ko daya, da ‘yan majalisun tarayya guda ishirin da hudu, babu mace ko daya. Banda gwamna da mataimaki, yace wannan manuniya ce cewa, har yanzu gwamnatocin Najeriya basu damawa da mata.
Da take bada tata gudummuwar, Maryam Garba Usman tace, mata suna da sha’awar shiga harkokin siyasa da kuma bada gudummuwa a fannin inganta rayuwar al’umma, sai dai galibi ba wadanda suka cancanta, wadanda kuma suke da kwarewa dama.
Ta jadada cewa, mata ne suka fi kusa da ‘ya’yansu sabili da haka sune suka fi dacewa da rike dukan mukaman da suka shafi ci gaban iyali.
Saurari cikakken shirin.
Your browser doesn’t support HTML5