Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adamawa: Yara mata biyu sun tada bam a Madagali


Wata 'yar kunar bakin wake a Madagali
Wata 'yar kunar bakin wake a Madagali

Wasu yara mata biyu sun tada bam cikin jama'a suka halaka mutane da dama tare da jikata wasu

Rahotanni sun tabbatar cewa wasu 'yan kunar bakin wake yara mata biyu suka tada bamabaman dake jikinsu a wani wajen hada-hadar jama'a inda kawo yanzu babu cikakken alkalumman wadanda suka rasa rayukansu ko suka jikata.

Wani ganao yace an samu hasarar rayuka da dama. Yace bam din farko da ya tashi ya kashe akalla mutane talatin da jikata wasu da yawa. Bam na biyun ita yarinyar da ta tada shi ya kashe.

Kwamandan rundunar soji dake kula da yankin Birgediya Victor Izegwu yace kawo yanzu suna cigaba da hada alkalumman hasarar rayuka da aka yi tare da cewa ba zasu yi kasa a gwuiwa ba wajen kare rayukan jama'a. Sojoji sun kwashe wadanda suka ji rauni zuwa asibitoci a Yola.

Hukumar bada agajin gaggawa ko NEMA tana tantance adadin wadanda suka rasa rayukansu.

Sabon harin na zuwa ne yayin da al'ummar yankin ke komawa gidajensu bayan kwatoshi daga hannun 'yan Boko Haram.

Wani mazaunin garin yace dole ne hankalinsu ya tashi.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG