DOMIN IYALI: Ma'anar 'Yancin Mata -Kashi Na Daya, Mayu 25, 2023

Alheri Grace Abdu

Ga wadanda su ke bibiyar shirin Domin Iyali, shirin ya haska fitika a kan batutuwa da dama da suka shafi mata. Kama daga rawar da suka taka a zabukan da ake gudanarwa a kasashensu, nasarori ko akasin haka da matan da suka tsaya takara suka samu, batun kashi talatin da biyar cikin dari na guraban siyasa da suke nema, da dai sauransu.

Wani batu da ya fita fili a dukan tattaunawar shine, ganin yadda har yanzu ake ci gaba da samun mabanbantan ra’ayoyi game da ‘yancin mata. Yayinda gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ke ban kwana, ta Bola Ahmed Tunubu kuma ke nade hannun riga ta kama aiki, tambayar ita ce? Menene makomar matan a sabuwar gwamnatin da za a kafa ranar Litinin.

Babu shakka, hakar mata ta ganin an dama da su ba zata iya cimma ruwa ba a kowacce gwamnati, sai idan wadanda su ke cikin gwamnatin sun fahimci ‘yancin da ake batu a kai.

Batun da shirin Domin Iyali zai fara haska fitila ke nan a wannan tattaunawar da wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari ya jagoranta.

Saurari kashin farko na tattaunawar:

Your browser doesn’t support HTML5

Ma'anar 'Yancin Mata, Kashi Na Daya