Washington, DC —
A shekara ta dubu biyu da goma sha biyar, Najeriya ta zartar da dokar haramta cin zarafin mutane da ake kira (VAPP), ciki har da cin zarafin mata, da cin zarafi a cikin gida. Bayanai na nuni da cewa, ya zuwa watan Satumbar 2024, jihohi 35 ne suka amince da dokar, ban da jihar Kano. Duk da yake dokar tana da tasiri, masu kula da lamura na cewa, za ta fi tasiri idan aka yi wadansu gyare-gyare yadda kwalliya zata iya biyan kudin sabulu. Yayinda wadansu ke kushewa dokar da yin kira a soke ta.
Saurari ci gaban tattaunawar:
Your browser doesn’t support HTML5