Washington, DC —
Daukar kananan yara su tashi a gaban wadansu da ba iyayen haihuwarsu ba ne, ba wani bakon abu ba ne a kasashen nahiyar Afrika, inda sau tari iyaye su kan nemarwa ‘ya’yansu mata da su ka yi aure, ‘yar daki da zata taimake su reno, ko kananan ayyuka ko aika a cikin gida. Sai dai wannan al’ada tana jefa yara da dama cikin mawuyacin halin rayuwa, sabili da cin zarafinsu da ake yi a gidajen, abinda sau tari, ya ke kai ga raunata su a wadansu lokuta ma har da rasa rai.
Shirin Domin Iyali ya yi nazarin wannan lamarin a wannan rahoto na musamman da wakiliyarmu Zainab Babaji ta hada mana.
Saurari cikakken shirin:
Your browser doesn’t support HTML5