DOMIN IYALI: Bibiya Kan Dokar Takaita Kayayyakin Aure A Gumel, Kashi Na Hudu, Yuli, 15, 2021

Alheri Grace Abdu

A ci gaba da neman fahimtar yadda dokar da aka kafa a Karamar Hukumar Gumel ta jihar Jigawa dake haramta yin kayayyakin aure da suke wuce kima zata amfani iyali, yau bakin da muka gayyata sun maida hankali kan tasirin dokar ga al'umma.

Bakin dai su ne Hon Salisu Abdullahi Gumel, sakataren cibiyar yaki da aikata miyagun laifuka a KRH Gumel da kwamred Yahaya Shu’aibu Ngogo dan gwaggwarmaya mai fafarukar kare hakkin iyali, da kuma Barrista Amina Umar Hussein sakatariyar kungiyar mata ta kasa da kasa FIDA reshen jihar Kano.

Saurari ci gaban bayanin Hon Salisu kan tasirin dokar. a tattaunawar da Mahmud Ibrahim Kwari ya jagoranta:

Your browser doesn’t support HTML5

DOMIN IYALI:Bibiya Kan Dokar Takaita Kayayyakin Aure A Gumel Kashi Na Hudu-10:00"