Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Bibiya Kan Dokar Takaita Kayayyakin Aure A Gumel, Kashi Na Uku, Yuli, 08, 2021


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

A ci gaba da bibiya kan dokar da aka kafa a Karamar Hukumar Gumel ta jihar Jigawa da ta haramta yin kayayyakin aure da suke wuce kima, yau bakin na mu sun maida hankali kan fassara abinda dokar kasa ta tanada da kuma yadda wannan dokar ta ke karo da waccan

Bakin da suka bakuncin wannan shirin, Hon Salisu Abdullahi Gumel, sakataren cibiyar yaki da aikata miyagun laifuka a Karamar Hukumar Gumel da kwamred Yahaya Shu’aibu Ngogo dan gwaggwarmaya mai fafarukar kare hakkin iyali, da kuma Barrista Amina Umar Hussein sakatariyar kungiyar mata ta kasa da kasa FIDA reshen jihar Kano.

Saurari tattaunawar da Mahmud Ibrahim Kwari ya jagoranta:

DOMIN IYALI:Bibiya Kan Dokar Takaita Kayayyakin Aure A Gumel Kashi Na Uku-10:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:34 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG