Dolly Parton Ta Lashe Kyautar Miliyan 100 Ta Jeff Bezos

Dolly Parton a shekarar 2019

‘Yar shekara 76, Parton wacce kan yi wakokin bege baya ga na Country, ta yi fitatttun wakoki irinsu, “I Will Always Love You,” “Jolene” da sauran zafafan wakoki da dama cikin gomman shekarun da suka gabata.

Fitacciyyar mawakiyar Country Music, Dolly Parton wacce har ila yau ta shahara a fannin taimakawa al’uma ta lashe kyautar “Bezos Courage & Civility Award” ta dala miliyan 100 da shugaban kamfanin dandalin kasuwancin yanar gizo na Amazon Jeff Bezos yake bayarwa.

“Bezos Courage & Civility Award,” kyauta ce da ake ba mutanen da suka yi zarra wajen “samarwa al’uma mafita” kan matsalolin da suke fuskanta, kamar yadda Bezos ya wallafa a shafin yanar gizo, a cewar Reuters.

Bezos wanda har ila yau shi ne mamallakin kamfanin nan na Blue Origin da ke zuwa kololuwar sararin samaniya, ya sanar da wannan kyauta ce a ranar Juma’a tare da abokiyarsa Lauren Sanchez.

Cikin wani sako da ta wallafa a shafin Instagram, Sanchez ta kwatanta Parton “a matsayin mace wacce ke da zuciyar kyauta da nuna kauna a duk ayyukanta.”

“Mun san za ki yi kyawawan aayyuka da wannan dala miliyan 100.” In ji Sanchez.

Wani hoton bidiyon bikin ba da kyautar da aka wallafa a yanar gizo, ya nuna Parton tana cike da mamaki kan waddannan kudade.

“Tirkashi! Dala miliyan 100 fa ka ce?” Parton ta tambaya cike da mamaki.

“Yana da muhimmanci mutanen da suke da ikon taimaka su rika yin hakan a inda zuciyarsu take. Zan iya bakin kokarina, wajen ganin na tafiyar da wadannan kudade ta hanyoyin da suka dace.” Parton ta ce.

‘Yar shekara 76, Parton wacce kan yi wakokin bege kuma marubiciya, ta yi fitatttun wakoki irinsu, “I Will Always Love You,” “Jolene” da sauran fitattun wakoki da dama cikin gomman shekarun da suka gabata.