Gwamnatin jihar Bauchi, a shiyyar Arewa maso Gabas ta bada sanarwar kafa dokar hana fita waje tun daga safiya har zuwa dare, biyo bayan kaddamar da hare hare da wasu ‘yan bindiga suka kaddamar a garuruwan Kirfi dakuma Alkaleri daya janyo asarar ran mutum guda.
sai dai tuni jam’iyar adawa ta APC tayi watsi da dokar, sanarwar da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin jihar da babban sakatare a gidan gwamnati mallam Abdullahi Lele, ya sanya wa hannu, tace dalilin barazanar tsaro da ake fuskanta ya zamo tilas gwamnan jihar Bauchi yakare rayuka da dukayar jama’ar jihar ta hanyar kafa dokar hana fita har sai jami’an tsaro sun shawo kan lamarin.
Sai dai tuni ‘dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC Barister Mohammed Abdullahi Abubakar, yayi watsi da dokar a wata hira da manema labarai dayayi, inda yace, “to mu abinda muke fadawa duniya shine, babu dalili da kodan da zai sa akafa wannan dokar ta baci, illa dai akwai wani nufi da ake dashi na kokarin canza sakamakon wannan zabe da karfin tsiya.”
Da alama dai dokar batayi tasiri ba domin kuwa jama’a sun fito inda sukayi ta kai kawo akan tutuna.