A Najeriya kungiyar motocin sufuri ta kasa wadda ta sanya hannu tsakanin ta da hukumar zabe mai zaman kanta INEC, cewar zata bayar da motoci da babura domin gudanar da ayyukan zabe, ta mayar da martani da kakkausan lafazi dan gane da zargin da hukumar zabe tayi mata, na cewar sune suka kasa bayar da motoci kuma suka kawo matsala a wasu yankunan da ba’a samu damar kai kayan zabe ba akan lokaci ranar Asabar.
‘Daya daga cikin shugabannin kungiyar motocin sufuri ta Najeriya, Alhaji Suleman ‘Dan Zaki, wanda tare da shi ne akayi wannan yarjejeniya tsakanin kungiyar da hukumar zabe, ya bayyanawa wakilin Muryar Amurka, cewa tilas ne hukumar zaben ta binciki kanta da kanta, saboda jami’an ta sune suka kawo wadannan matsalolin.
Alhaji Suleman dai yace kungiyar sa tayi duk ayyukan da ta dauki alkawarin yi, yakuma ce ko a Katsina an kai motoci amma aka ce ba’a bukatar motocin haka a jihar Nija, a kaduna kuma shugaban ne yayi amfani da motar sa wajen kai kayayyakin zabe domin tabbatar da cewa ba’a samu wata matsala ba akan wannan yarjejeniyar.