Dokar Raba Gado Daidai Tsakanin Maza da Mata Ba Zata Yiwu Ba A Najeriya

Ginin majalisun tarayyar Najeriya

Shugaban kwamitin labarai na majalisar dattawan Najeriya Sanata Aliyu Sadi Abdullahi yace zata yi wuya majalisar ta amince da kudurin dokar daidaita rabon gado tsakanin maza da mata a Najeriya

Kudurin dokar neman a kawo daidaito tsakanin maza da mata a rabon gado ba sabon abu ba ne domin inji shi Sanata Sadi Abdullahi an taba gabatar dashi kafin majalisar tayi watsi da kudurin

Sanata Abdullahi yace sun yi watsi da dokar domin akwai wuraren da ta sabawa 'yancin 'yan kasar. Kodayake dokar na kokarin kwato 'yanci ne amma kuma a wani gefen ta tauyewa mutane 'yancinsu.

Dokar bata zo daidai da addinin musulunci ba kuma hatta kiristoci ma sun ce basa son dokar,inji Sanata Abdullahi. To saidai za'a ba 'yan kasar damar duba dokar a bainar jama'a su tofa albarkacin bakinsu.

A wani hannun kuma tuni kungiyoyin addinin musulunci suka dukufa wajen fafutikar ganin majalisar tayi watsi da kudurin bisa ga dalilin cewa dokar ta sabawa koyaswar addinin musulunci kamar yadda shugaban IZALA Shaikh Bala Lau ya bayyana. Yace kada sanatoci musulmai su yadda ma a yi maganar.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Dokar Raba Gado Daidai Tsakanin Maza da Mata Ba Zata Yiwu Ba A Najeriya - 2' 57"