To sai dai kuma, batun da a yanzu haka ya soma jawo cece-kuce,inda wasu ke yabawa da wannan mataki, yayin da wasu kuma musamman wadanda abun ya shafa ke kokawa.
Ba tun yau ake kai ruwa rana game da cunkuson ababen hawa a babbar kasuwan garin Jalingon ba, musamma ta titin fada wato palace way, wanda itace babbar hanyar da ta hada kasuwar da kuma wasu sassan fadar jihar.
Kuma don magance wannan matsalar cunkuson dake jawo hadurra da kuma ke barazana ga harkar tsaro yasa mahukunta a jihar suka kafa dokar hana kasa kaya ko kuma ajiye ababen hawa inda tuni har dogarawan aiki da cikawa wato yan ‘’Task Force’’ suka fara aikin ba sani ba sabo,domin tsaftace birnin.
Batun dai a yanzu haka ya soma jawo cece-kuce,inda wasu ke yabawa da wannan mataki, yayin da wasu kuma musamman wadanda abun ya shafa ke kokawa. To sai dai kuma yayin da wadansu ke kokawa da alamun wasu na ganin matakin yayi dai-dai.
Hukumomin jihar dai sun ce kafin daukar wannan mataki sai da aka tattauna da shugabanin kungiyoyin 'yan kasuwa dana direbobi dama na 'yan acaba domin baiwa kowa hakkinsa.
Hon Nasiru Bobboji,dake zama shugaban riko na karamar hukumar Jalingon, ya bayyana matakan da suka dauka kafin aiwatar da wannan doka.
Masu fashin baki dai na ganin sake fasalin tsarin sufuri a birnin Jalingon fadar jihar a matsayin babban matakin rage cunkoson ababen hawa da kuma hayaniyar da ake fuskanta wanda a kullum hukumomi a jihar ke saba layar kaiwa kamar yadda shugaban rikon na Jalingon yayi Karin haske.
Ga rahoton Ibrahim Abdul’Aziz.
Your browser doesn’t support HTML5