A shekara ta 2019 da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu ga dokar kare hakki da inganta jin dadin mutane masu lalura ta musamman, inda suka kasance cikin farin ciki saboda tunanin cewa zasu samu saukin rayuwa.
Sai dai kawo yanzu saka hannu ga dokar ya kasa yin tasiri da za'a ce madalla, domin da yawa gwamnatocin jihohi sun ki aiwatar da dokar.
A hirar shi a Muryar Amurka, Haliru Shehu Usman jami'in gudanarwa na hadaddiyar kungiyar makafi a yankin arewa maso yamma yace daga cikin jihohin yankin su bakwai jihar Sakkwato da Kaduna ne kadai suka samar da dokokin suma kuma suna tattare da kalubale.
Masu kula da lamura na cewa, aiwatar da dokar yadda ya kamata, zai sa masu wannan lalura su samu sauki a haujin neman ilimi, samun aikin gwamnati da ma samun shiga gine gine na hukuma cikin sauki.
A haujin kiyon lafiya ma masu lallura na fuskantar matsaloli kamar wajen hawan gado ga maras lafiya gurgu ko kuma maras lafiya kurma da basu iya bayani ga ma'aikatan lafiya kuma babu wani tanadi da aka yi musu.
Bisa ga bayanin su, lokaci daya da masu wannan lallura ke samun kulawa shi ne lokacin siyasa.
Shugaban kungiyar makafi na arewa maso yamma Haliru S Usman yace hukumar zabe na kulawa da bukatun su wajen jefa kuri'a ko yin rijistar Katin zabe amma wajen aiwatar musu ayukan samun romon dimokradiya sai a ware su gefe, ba su sanin inda zasu same shi, balle dokokin kare hakkin su.
Duk da hakan mahukunta na sane da cewa wadannan mutane da aka kiyasta adadinsu ya kai sama da biliyan 25 a Najeriya, suna da muhimmanci a cikin al'umma.
Kamar yadda gwamnan Sakkwato ya fada wani lokaci da yake zantawa da su, akan kafa hukuma mai kula da bukatun su inda yake bayani akan basira da hazakar da Allah ya ba wasu daga cikin su, fiye da wasu mutane masu lafiya.
Masu wannan lalura na tunatar da gwamnatoci akan su sani kulawa da bukatun su hakki ne ba yi musu gata ba ne.
Zaunab Sa'idu Abdulnasir tace ba maganar tausaya musu ba ne, batun bin doka ne, kuma duk abubuwan da suke bukatar a samar musu ba su kadai zasu amfana ba, kowa na iya samun kansa cikin lalurar da suke da ita, domin akwai rashin lafiya akwai tsufa mutum na iya rasa idanu ko kunnuwa ko kafafu.
Ko jihohin da suka aiwatar da doka, masu lalurar sun ce akwai rangwame ga yadda ake kula da su, kuma da an bi tanadin dokar sau da kafa da an kawo karshen matsalolin su kowa ya huta.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5