Wakilin Muryar Amurka dake Maiduguri babban Birnin jihar Borno, Haruna Dauda Biu ya yi kicibis da wasu cikin nakasassun, walau suna kan kekunan guragu ko suna dauke da sanduna ko ja da gindi, suna share tituna.
Nakasassun na sanye da wasu kaya na musamman da hukumar tsaftace muhalli ta basu.
A tattaunawar da Haruna Dauda ya yi, Muhammad Abubakar ya shaida mashi cewa duk wani mai lallura ana ganin tamkar mabaraci ne amma su barar ta fita daga ransu, masu kafa ne yanzu suke bara. Dalili ke nan da suka nemi aikin da masu kafa basa son yi.
Alhaji Abdulrahaman Kwankwasiya wanda shi ma nakasasshe ne ya ce ya yi matukar murna da samun aikin.
Alfaki Idris shugaban guragun jihar Borno yace kamar yadda ake biyan duk wani ma’aikacin tsaftace muhalli Naira dubu goma kowane wata, haka su ma ake biyansu. Ya roki gwamnan jihar Kashim Shettima da ya mayar dasu ma’aikatan din-din-din.
Shugaban hukumar tsaftace muhalli ta jihar Alhaji Nasiru Ali ya bayyana dalilin da ya sa suka dauki guragun aiki. Yace rikicin Boko Haram ya sa mutane da yawa sun rasa abun yi duk da bukatar dake akwai na karewa kowa hakkinsa ya sa aka dauki nakasassun aiki. Kawo yanzu hukumar ta dauki nakasassun 30 cikin su 60 da suka nemi aikin. Yace za’a sa sauran cikin kasafin kudin sabuwar shekara domin su ma a daukesu aiki
Haruna Dauda na da karin bayani
Facebook Forum