Dokar Hana Anfani Da Leda Ta Fara Aiki A Kasar India

Firayin Ministan kasar India, ya dauki kwakkwaran matakin dakile amfani da leda da robobi domin shawo kan gurbatar muhalli.

Manyan shaguna da gidajen sayar da abinci da masu sayar da kaya bisa hanya, a Mumbai dake kasar India na korafe korafe akan dokar gwamnati ta dakatar da amfani da leda da robobi a birni mafi girma a kasar Indiya.

Yayin da tawagar masu bincike 200 suka bazama cikin garin mai jama’a miliyan 20, domin aiwatar da dokar, sun sami shagunan sayar da abinci na Burger King, da McDonald da kuma shagon sayar da coffee na starbucks na cikin da dama da aka samu da laifi.

Dokar a jihar Maharashtra, da Mumbai shine babban birnin kasar, ta sami lambar yabo daga wadanda bada gargadin cewa zubda ledoji da robobi a ciki da wajen biranen India, dake toshe magudanan ruwa da rafuka, ya haifar da babbar barazana ga muhalli.

Amma kamfanin ledoji da robobi ya soki lamarin da cewa yin hakan zai raba mutane dubu 300, da ayyukan su.

Dokar hana zubda ledoji da robobi ta fara aiki ne makwanni kadan bayan firayin minister Narendra Modi, ya sha alwashin kawo karshen amfani da ledoji a shekarar 2022, domin kasancewa kan gaba a duniya wajan rage amfani da leda.