Najeriya na da yawan arzikin iskar gas a duniya. Sai dai da wasu gidajen mai na CNG da ake da su a kasar, da yawa wadanda suka canza motocin na fuskantar wani sabon kalubale.
Ganin dogayen layukan motoci masu tsayin daruruwan mitoci suna jiran shan man fetur ba sabon abu bane a Najeriya.
Amma wannan ya bambanta. Anan, matafiya ne ke fatan samun iskar gas a daya daga cikin yan cibiyoyi da ke rarraba CNG a fadin kasar.
Wasu kamar Yahaya Ibrahim, sun shafe kwanaki biyar suna jiran samun wannan makamashi.
Yahaya ya ce, “Bayan da na sauke kaya a jihar Katsina, na zo nan ne saboda sauran iskar gas ba za ta mayar da ni jihar Kogi ba, inda na fito.”
Shima direban tasi Abdullahi Ashiru, ya canza motarsa watanni uku da suka wuce, kuma yana kashe kashi uku kacal na kudin man fetur da yake amfani da shi kullun don aiki da iskar gas.
Sai dai ya ce fafutukar samun CNG a baya-bayan nan abin takaici ne.
Abdullahi ya ce “Na zo nan tun karfe 11 na safe, yanzu karfe nawa kenan? Kusan karfe 4 na yamma ne kawai saboda ina kokarin siyan CNG?”
Najeriya ce ke da mafi yawan iskar gas a Afirka, kimanin kamu triliyan 209.
Kuma a shekarar da ta gabata, jim kadan bayan janye tallafin man fetur, gwamnatin kasar ta kaddamar da wani shiri mai karfi na komawa amfani da makamashi mai tsafta, ciki har da shirin samar da motoci miliyan 1 masu amfani da iskar gas ko CNG a kan tituna cikin shekaru uku.
Makamashi mai tsafta kamar Iskar gas shine mafi arha da tsafta madadin man fetur ga 'yan Najeriya.
Amma hukumomi a Najeriya sun ce akwai tashoshin samar da iskar gas kusan 50, ga ‘yan Najeriya sama da miliyan 200 da ke kokarin maye gurbin makamashi mai tsada kamar man fetur da dizal.
Farashin man fetur ya karu da kusan ninki shida tun bayan da gwamnati ta yi watsi da shirin tallafin da ta ke yi a bara, lamarin da ya sa mutane da dama ke sha'awar sauya sheka zuwa iskar gas.
A halin yanzu akwai kusan cibiyoyin dake sauya injinan motocin 130, kuma hukumomi suna da niyyar kafa karin daruruwa a duk fadin kasar nan da 2027.
Amma da yawa kamar Omotayo James mazaunin Abuja sun ce babu bukatar hakan, idan har ba za a iya samun isasshiyar iskar gas din ba.
A watan da ya gabata, gwamnati ta ba da sanarwar wani shiri na tara dala miliyan 250 nan da shekarar 2027 don tallafawa ci gaban ayyukan samar da iskar gas ko CNG.
Amma da yawa sun ce har yanzu suna matukar bukatar samar da makamashin.