Direbobin Motocin Sufuri Sun yi Yajin Aiki a Jamhuriyar Niger

Shugaba Mouhammadou Issouffou, Jamhuriyar Nijer

A Jamhuriyar Niger direbobin motocin sufuri sun yi yajin aiki lamarin da ya saka mutane cikin wani mawuyacin hali
Yajin aikin na kwana daya da motocin sufuri suka yi ya kumshi ilahirin duk motocin dake zirga-zirga lamarin da ya saka jama'a cikin wani mugun hali domin rashin iya zuwa wuraren ayyukansu na yau da kullum.

Wasu da aka zanta dasu a kan hanyarsu ta zuwa asibiti sun rasa motar da zata kaisu tun safe sai wahala sukai ta yi. Yajin aikin ya sami mutane ba zata, wato babu wanda ya san direbobin zasu yi yajin aiki. Masu son fita zuwa wasu garuruwa kuma su ma lamarin ya rutsa da su.

A wata unguwar dake bayan tsakiyar birnin Niamey wani Malam Umaru wanda ya dade ya na jiran mota ya ce yajin aikin ya takurashi sosai. Yajin aikin ya kutunta masa domin ya kasa zuwa neman abun rayuwar na yau da kullum.

Alhaji Ibrahim Akwara shugaban kungiyar direbobin motocin sufuri na Jamhuriyar Niger ya ce dalili na daya da ya sa suka shiga yajin aiki shi ne rashin man fetur. Abu na biyu ita ce matsalar da suke samu tsakaninsu da 'yansanda da jandarmomi da duwan. Dalili na uku shi ne matsalar da suke da shi tsakaninsu da motocin dake daukan mai. Dalili na hudu shi ne yawan haraji a cikin birnin Niamey da ma kasa gaba daya.

Domin rage zafin yajin aikin ya sa gwamnati ta tanadi motocin safa-safa na daukan fasinjoji zuwa guraben aikin yi.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Direbobin Motocin Sufuri Sun yi Yajin Aiki a Jamhuriyar Niger - 3:30