Dimokradiyar Congo Ta Samu Sabon Firayim Minista

Joseph Kabila shugaban kasar Dimokradiyar Congo

Shugaba Joseph Kabila na Junhuriyar Demokradiyar Congo ya nada wa kasar sabon Firayim.Ministan

Wanda kuma aka nadan wani babbar kusar ‘yan adawa ne mai suna Badibanga Ntita Samy, wanda kuma shine zai ja ragamar gwamnatin gamin-gambiza ta Congo din har zuwa lokacinda aka gudanar da zaben nan da aka jinkirta gudanarwa.

Wannan zaben da ya kamata a yi shi a cikin watan nan na Nuwamba, yanzu an dage shi har sai zuwa watan Aprilun shekarar 2018.

A cikin wannan makon ne gwamnatin ta Kabila tace ta yi murabus a karkashin wata yarjejeniyar da aka kulla da wani bangare na jam’iyyun adawa da suka yarda shi Kabila din ya ci gaba da zamansa a kan karagar mulki, watau yayi ta-zarcen wuce wa’adinsa na biyu na mulki.

Sai dai kuma wata gamayyar jam’iyyun ‘yan adawa ta daban ta nemi shugaba Kabila ya sauka ran 19 ga watan Disamba, ranar da ya kamata wa’adin mulkinsa na biyu, ya kare.