Firayim Ministan Junhuriyar Demokradiyar Congo yayi murabus.
A jiya ne Augustin Matata Ponyo ya ajiye mukamin nasa a bisa yarjejeniyar siyasa da aka shata don tsawaita wa’adin mulkin shugaban kasar Joseph Kabila da kuma kauce wa tarzomar siyasa.
A karkashin yarjejeniyar da Kungiyar Kasashen Afrika ta A-U ta baiwa goyon baya ne aka ajiye cewa shugaba Kabila zai ci gaba da mulki har zuwa shekarar 2018 lokacinda za’a gudanarda zabe, duk da cewa a watan Disambar wannan shekara ya kamata wa’adinsa ya kare.
Shugaba Jose Eduardo Dos Santos na Angola, wanda shima tun shekarar 1979 yake kan karagar mulki, yace wannan yarjejeniyar zata bada damar a gujewa jayayya akan sha’nin mulki a kasar ta Congo.