Tsohon Firai Ministan Birtaniya David Cameron ya bada sanarwar yin murabus daga kujerarsa ta majalisar dokoki, abin da zai kawo karshen harkokin siyasarsa, makwanni bayan da ya sha kasa a zaben raba gardama na ranar 23 ga watan Yuni na neman zama ko ficewar kasar daga kungiyar Taryyar Turai.
WASHINGTON, DC —
Lokacin da Cameron, dan shekaru 49 da haihuwa, ya gabatar da takardan murabus a matsayin Prime Minstan ya bayyana niyyarsa na ci gaba da zama a majlisar koda yake ba rike shugabancin jami’aiyarsa ta Conservative ba.
Cameron yace ya shaidawa sabuwar Farai Minista Theresa May, cewa zai daina wakiltan mazabarsa a Oxfordshire don ya bada dama ga wani maye gurbinsa akan kujeran, wanda zai mai da hankali a kan yankin dake tsakiyar Ingila.
Sanarwar bazata da Cameron yayi, ana sa ran zai sa a gudanar da zaben cike gurbi na kujeransa ta mazabar Oxfordshire.