Jiya Litini Kwamitin ya nuna alamar yana shirin ya dauki matakin ladabtarwa kan Koriya Ta Arewa saboda abin da Kwamitin ya kira, "halin bijirewa mai cike da tsokana" game da bukatar tun farko ta cewa ta kawo karshen duk wani shiri na makamin nukiliya.
A wani bayanin hadin gwiwa, wanda kasar China, ta goyi bayansa, Kwamitin ya bayyana abin da ya kira, "matukar damuwa" game da kaddamar da gwajin da Koriya Ta Arewa ta yi ranar Lahadi, wanda Koriya Ta Arewar ta kira makami mai linzami na tsaka-tsakin zango wanda ya yi tafiyar tsawon kilomita 787 kafin ya fada cikin kogin Japan.
Hurucin Kwamitin ya bayyana kaddamar da wannan makamin da "take-take mai matukar janyo tashin hankali" da ke cigaba da tayar da jijiyoyin wuya a yankin Gabashin Asiya da sauran wurare. Sannan Kwamitin ya yi kira ga dukkan kasashe da su aiwatar da dukkan nau'uka shida na takunkumin da aka kakaba ma Koriya Ta Arewar, wadanda tuni ma majalisar dinkin duniya ta shiga aiwatarwa.