Daukaka Na Zuwa A Duk Lokacin Da Mace Ta Mutunta Kanta

Maryam Kassim Muhammad

Maryam Kassim Muhammad, wata matashiya mai sana’ar sayar da Haja da Turaren kamshi, na kasar Sudan don sayarwa mata a gidajen su.

Maryam ta fara sana’ar hannu shekaru biyu da suka wuce a lokacin da ta ke karantun ta na digiri, domin zamo mai dogaro da kai, ta fara sana’ar turaren wuta ne sanadiyar son kamshi da yawaita sayan turaren na wuta.

Hakan yasa ta je ta koyi yadda ake saraffa turaren wuta na Sudan domin sayarwa amare da 'yan mata.

Sana’ar hannu da malama Maryam ta ke yi ta ce baya takurawa harkar karatunta, sannan ta na amfani da shafin sadarwa wajen tallata hajarta, sannan mafi yawan lokuta daga kayan da ta ke sakawa na yau da kullun da zarar an gani a jikinta sai ta samu kasuwa a wajen mata masu son kawa.

Babban abin da ke ci mata tuwo a kwarya bai wuce bashi da rashin son biya a kan lokaci, mussaman ma ga mata, ko da yake akan samu taurine bashi a bangaren maza ma a wasu lokuttan.

Daga karshe ta ja hankalin 'yan uwanta matasa da su jajirce su zamo masu dogaro da kai.

Your browser doesn’t support HTML5

Daukaka Na Zuwa A Duk Lokacin Da Mace Ta Mutunta Kanta 5'50"