Dattawan Jihar Kano Sun Bukaci 'Yan Sanda Su Binciki Gwamna Ganduje

Dr. Abdullahi Umar Ganduje gwamnan Kano

Wasu Dattawa a jihar Kano sun yi kira da babbar murya ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya fito yayi wa mutanan kano bayani akan faifan bidiyo da ake zargin ya nuna shi yana karbar cin hanci daga gurin yan kwangila.

Kimanin makonni biyu bayan da babbar kotun Kano, ta haramtawa Majalisar dokokin Jihar bincikar faifen bidiyon dake zargin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, yana karbar cin hancin dala miliyan biyar, dattawan Kano sunce akwai bukatar gwamnan ya yiwa al'umar jihar bayani da zai gamsar da su game da zargin.

Hakan dai na zuwa a dai-dai lokacin da jama'a ke korafi kan yadda dattawan na Kano suka ki cewa uffan tun bayan da Jaridar Daily Nigeria ta fara kwarmata zargin karbar rashawar akan gwamna Ganduje.

Daya daga cikin dattawan Jihar Kano, Alhaji Gidado Mukhtar, yace abu na farko da ya sa dattawan ba su yi magana ba shine domin maganar tana gaban kotu, da bisa doka bai kamata a saurara, na biyu kuma magana irin wannan idan ta taso ya mata a tsaya a ga inda ta gangara kafin aga mene ne a ciki.

Gidado yakara da cewa tunda kotu tayi hukunci ‘yan sanda suna da hakki da kuma damar su bincika wannan zargi da ake yiwa gwamna Abdullahi Umar Ganduje, yanzu suna sauraron ‘yan sanda su yi aikin daya kamata wajen bincikar wannan zargin karbar cin hancin.

Ga wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari da cikakken rahoton

Your browser doesn’t support HTML5

Dattawan Jihar Kano Sun Bukaci Yan Sanda Su Binciki Gwamna Abdullahi Ganduje