A Najeriya, daruruwan mata daga dukkan jihohi 36 na kasar ne suka kwashe kwanaki uku suna wani taro na musamman a dakin taro na cibiyar mata da ke Abuja wanda suka yi wa lakabi da "The Nigeria We Want" wato "Irin Najeriyar Da Muke So".
Matan sun yi ta rera wakar da ta zama taken mata inda suka bayyana bukatunsu na samun 'yanci da walwala.
Abin da ya dauki hankali a taron shi ne, batun cewa sun bar neman kashi 50 cikin 100 na mukamai ko a gwamnatance, ko a siyasance, inda suka koma neman kashi 35 cikin 100.
Daya daga cikin shugabannin da suka shirya taron, Madam Ene Ede, ta ce sun cimma matsayar ne domin ba sa samun yadda suke so a duk lokacin da aka ce ana yin wani abu da zai ciyar da kasa gaba.
Ita kuwa ministar ma'aikatar mata ta kasa, Dame Pauline Talen, ta yaba tare da nuna goyon bayanta ga yunkurin da mata suka yi wajen hada kansu wuri guda saboda su samu ci gaba mai dorewa a harkokinsu.
Wasu mata da suka halarci taron daga jihohi daban-daban irinsu Jihohin Kaduna, Zamfara, Bauchi, sun koka akan harkar tabarbarewar tsaro da ke shafar su da 'ya'yansu.
Abin jira a gani shi ne irin tasirin da hadin kansu zai haifar masu.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5