Gabanin karshen ziyarar da ta kai Abujan Nigeria tare da tawagar ta, Shugabar Muryar Amurka Amanda Bennett ta gana da shugabanin kungiyoyin masu sauraren Sashen Hausa na Muryar Amurka a Abuja.
Kakakin kungiyar masu sauraren gidan rediyon ya bukaci Muryar Amurka ta gayyacesu wata rana lokacin wani buki su zo nan Birnin Washington DC idan ta yiwu ma su ziyarci Fadar White House.
Shugabar kungiyar dake hana kangarewar yara Halima Baba Ahmed ta bukaci Muryar Amurka ta fito da shirin ilimin mata zalla. Kazalika ‘yar siyasa Zainab Bununu tana cikin masu sauraron. Ta ce idan aka ware wata sana’a aka ce mata ba zasu yi ba cutuwa a wurinsu mata.
Shi ko Hassan Abdullahi y ace suna alfahari da gidan rediyon Muryar Amurka. Shima Adamu Abdullahi ya nuna murnarsa akan ganawa da Amanda Bennett. Sani Kafinta cewa ya yi kullun sai sun saurari Muryar Amurka saboda haka sun ji dadin ziyararta.Sambo Jibrin Jada yace ziyarar ta Amanda Bennett ta nuna akwai dankon zumunci mai kwari tsakanin Nigeria da Amurka.
Yau Yakubu Yobe ya roki Amanda Bennett ta amsa kokensu na ganin wasunsu sun ziyarci Amurka domin su gani da idanunsu yadda ake gudanar da abubuwa a gidan rediyon Muryar Amurka.
Shugaban kungiyar Buhari ya yabawa gidan rediyon bisa kokarin da ya keyi wajen fitar da labaran Gaskiya dake taimakawa matuka. Ya yi misali da yadda rediyon ya bada wasu bayanai akan wasu jami’an sojoji da ba’a biyansu hakkinsu. Rahoton gidan rediyon ne ya taimaka ya fadakar da duniya har aka biyasu.
A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da jin karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5