Darajar Naira Ta Cira Karon Farko Bana

Sabbin kudin Naira

Tsawon mako 2 kenan da kudin Naira ke samun tagomashi a kasuwar musayar kudade a kasar, inda ake musayar kudin akan kasa da Naira 1,570 a kowacce dalar Amurka, maimakon Naira 1,740 da yake a baya, kuma wannan shine karo na farko da kudin Naira ya samu irin wannan tagomashi a shekarar 2024.

Masana tattalin arziki na ganin sabbin tsare-tsaren da babban Bankin kasar (CBN) ya fito da shi wajen mayar da musayar kudaden ta intanet mai suna Electronic Foreign Exchange Matching System ko kuma (EFEMS), da kuma yawaitar dalar Amurka a kasuwar musayar canji, na daga cikin dalilan da yasa Naira ke cigaba da samun daraja.

Sai dai 'Ƴan kasar na bayyana cewa, su basu ga alfanun tagomashin da kudin kasar ke samu ba, domin har yanzu farashin kayayyaki a kasar na cigaba da hauhawa.

Dakta Bature Abdulaziz MON, wanda shine shugaban ƴan kasuwa a Najeriya, ya shaida wa Muryar Amurka cewa, “ba lallai bane darajar da kudin Naira ke samu ya sauke farashin kayayyaki a kasar ba, domin kayayyakin da suke kasuwa yanzu, tsoffin kaya ne”.

Abdulaziz, ya kara da cewa, “suna daukar tsawon kwanaki 50 kafin su samu sabbin kayayyaki”.

Masana dai na ganin darajar da Naira ke samu a yanzu na wucin gadi ne, idan har gwamnati ba ta jajirce akan matakan da ta dauka ba.

'Ƴan kasar dai na cigaba da hankoron ganin yadda gwamnatin kasar za ta shawo kan matsalar tattalin arziki da ƴan kasar ke fama da shi.

Saurari cikakken rahoton Rukaiya Basha:

Your browser doesn’t support HTML5

Darajar Naira Ta Cira Karon Farko Bana