Babban bankin Najeriya ne ya gudanar da wannan binciken, inda ya gano cewar matsalar wutar lantarki itace babbar damuwa ga hada hadar tattalin arziki a Najeriya. sauran matsalolin sun hada da matsalar kudi da yawan kudin ruwa da rashin kyakkyawan yanayin hada hadar kasuwanci da kuma rashin kyakkyawan dokokin tattalin arziki.
Sai dai wani masani kuma mai sharshi kan al’amuran yau da kullum Baba Yola Mohammdu Tanko, na ganin wannan ra’ayin babban bankin Najeriya ne kawai, domin idan gwamnati kara matse shigowa da kayayyaki daga kasashen waje da ci gaba da yin amfani kayan da ake dasu a cikin gida, wanda hakan zai dakile tashin Dalar.
Shi kuma masanin tattalin arziki Yusha’u Aliyu, na ganin idan har gwamnati zata shigo da abincin da zai taimakawa kasuwa da dai dai ta farashi ta yadda mutane zasu iya saya. Domin duk wannan matsala ta farune domin wasu ‘yan kasuwa na boye abinci da kuma kulle kasuwa da akayi wanda tattalin arzikin kasar ya dogara a kanta.
Saurari cikakken rahotan Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5