Idan kudurin ya zama doka za'a rage shekarun neman zama shugaban kasa daga arba'in zuwa talatin.
Kazalika wanda yake neman kujerar gwamnan za'a rage daga shekaru talatin da biyar zuwa talatin. Na 'yan majalisun tarayya da na jihohi a rage daga talatin zuwa ishirin da biyar.
Abdullahi Umar Faruk dan majalisar wakilai ne kuma ya amince da yunkurin amma ya kira a yi kokari a jawo matasa cikin lamarin saboda yana ganin yin hakan cigaba ne.
Bashir Muhammad Baba mai nazari akan alamuran yau da kullum na ganin yin hakan wani abu ne mai kyau saboda ko ba komi zai kawo zaman lafiya a kasar. Yace Najeriya kasa ce mai tasowa kuma a kasa irinta gwamnati ce uwa mai ba da mama. Baicin hakan matasa su ne kashi saba'in cikin dari na yawan al'ummar kasar. Idan aka dakilesu ba'a basu dama ba to gaskiya ba za'a zauna lafiya ba, inji Bashir.
Bashir ya yi misali da matasan da suka taba rike mukaman shugabanci a kasar. Misali Janar Yakubu Gowon yana dan shekaru ishirin da takwas, kuma ko aure bai yi ba ya zama shugaban kasa.Irinsu Shehu Shagari, su Yusuf Maitama Sule duk suna matasa suka rike mukaman siyasa.
Ita ma shugabar kungiyar kare 'yan mata 'yan siyasa Mercy Onyekwelu tace idan za'a yi dokar kuma zata dore to tana tare da 'yan majalisun dari bisa dari saboda kasashen dake ba matasa dama suna cigaba sosai.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.