Dangote Zai Jagoranci Yaki Da Zazzabin Cizon Sauro

End Malaria Council Abuja

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da kwamiti na musamman mai mutum 16 don kawo karshen zazzabin cizon sauro a kasar karkashin jagorancin attajiri Alhaji Aliko Dangote.

Hakan ya biyo bayan shawarar da Kungiyar Tarayyar Afrika ta bayar na cewa ya kamata duk kasashen Afrika su kafa kwamitin don kawo karshen zazzabin cizon sauro dake barazana ga rayuwar yara musamman ‘yan kasa da shekaru biyar da mata masu juna biyu.

Shugaba Buhari ya ce ya zabi Alhaji Aliko Dangote ne a matsayin shugaban kwamitin duba da irin gudumawa, nasarori da kuma tallafawa ayyuka daban-daban da suka shafi kiwon lafiya kamar cutar polio da kuma karfafa tsarin kiwon lafiya a matakin farko.

End Malaria Council Nigeria

Buhari, wanda ya nuna damuwa game da rahoton Majalisar Dinkin Duniya na shekarar 2021 dake nuna cewa kashi 27 cikin dari na al’ummar kasar na fama zazzabin cizon sauro yayin da kasar keda kashi 32 cikin dari na yawan masu mutuwa sakamakon cutar a fadin duniya.

Shugaban ya ce kawo karshen zazzabin cizon sauro a kasar zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin kasa da kimmanin naira biliyan 687 a shekarar 2022 da kuma naira tiriliyan 2 zuwa shekarar 2030.

End Malaria Council

Daraktan tsare-tsare, bincike da kididdiga na hukumar lafiya matakin farko a Abuja Dakta Abdullahi Bulama Garba ya ce sai mutane sun bada hadin kai don kawo karshen cutar.

Babban jami’in kiwon lafiya Dakta Hassan Shu’aibu ya ce kafa kwamitin abune mai kyau tare da fatan al’ummar Najeriya zasu amfana da matakin.

Idan za’a iya tunawa, a farkon watan Mayu wannan shekarar ne kasar ta ce zata karbi allurar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro nan bada jimawan ba.

Saurari cikakken rahoton Hauwa Umar daga Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

Dangote Zai Jagoranci Yaki Da Zazzabin Cizon Sauro.mp3