Ganin yadda babbar jami’ar Ibadan ta kasance bata da ginin makarantar koyon kasuwanci, ya sa Dangote yayi musu alkawarin tallafawa da zunzurutun kudi har Naira Milayan 250, amma sai gashi ya yi wannan aiki da kudinsa ya kai Miliyan 400.
Makarantar dai za ta taimaka wajen koyar da darusa tare da bada horo kan ilimin ksauwanci da dogaro da kai.
Daya daga cikin shugabannin kamfanin Dangote a kasashen Afirka, Zuwaira Yusuf, ta tabbatar da cewa an kayata cikin ginin da duk wasu abubuwan da ake bukata.
Haka kuma Zuwaira ta yi kira ga malaman da daliban jami’ar da su amfani da wannna makaranta ta hanyar da ta kamata.
A nashi jawabin da ya yi shugaban jami’ar Ibadan Farfesa Idowu Olayinka, ya nuna godiya ga Alhaji Aliko Dangote, bisa ga gina wannna cibiya da zata taimakawa malamai da dalibai.
Ita dai wannan cibiya ta kunshi babban dakin koyarwa da ofisoshi da ajijuwa da kuma dakin karatu da babban kanti. Haka kuma an saka na’urorin sanyaya dakuna da kuma babban injin dake bayar da wutar lantarki.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Umaru Tambuwal.
Your browser doesn’t support HTML5