Treloli goma sha shidda, cike da kayan abinci, da na masarufi wanda a
cewar Gwamnan jihar Maradi Zakari Umaru, ya tashi kimanin million dari
ukku na sefa. Ya kara da cewa, da ma akwai irin su PAM, da HCR, da Gwamnan Sokkoto, da NEMA ta Najeriya dake taimaka musu, kuma an yi musu rijiyoyi sannan ana basu magunguna.
Yanzu haka dai babbar damuwar su, har ma da 'yan gudun hijiran, ingantaccen tsaro ya dawo domin su koma garuruwan su. Wannan shine dalilin da yasa Gwamna Zakari, ya rubuta wa hukumomin yankunan Najeriya wasiku domin su zauna, su samo mafita.
Su ma bayan godiya 'yan gudun hijiran, sun bayanna wa wakiliyar Muryar Amurka Tamar Abari, fatan su na komawa cikin 'yan uwansu, da garuruwansu na ainahi.
A saurari cikakken rahoton daga wakiliyar Muryar Amurka Tamar Abari.
Your browser doesn’t support HTML5