Sabuwar dokar kasar ta bada damar cewa duk wanda zai tsaya takara to wajibi ne ya mallaki takar shaida karatu mafi karanci mai mataki 12, ko kuma kwatankwacin sa.
Kafin ya koma cikin jamiyyar adawa ta UNDP, Mwanba dai shine ministan tsaro, kuma daya daga cikin manya-manyan masu mara wa jamiyya mai mulki PF baya da karfin aljihun sa.
Sai dai da dangantaka tayi tsami ne, magoya bayan jam’iyyar PF suke cewa Mwanba baya da cikakkun takardun da dokar kasa ta tanada,
Suka ce daya daga cikin dalilan daya sa ya bar jam’iyyar kenan domin ya kasa bada takardan shaidan sa na karatu ga jami’yyar, wanda yana daya daga cikin sharuddan jam’iyyar domin ta tabbatar cewa duka ‘ya’yanta da zasu tsaya takara basu da matsala.
Sai dai mai magana da yawun jamiyyar adawa ta UNDP Charles Kakoma yayi watsi da wannan zargin, yana cewa ba kome bane illa neman suna tare da neman kuria’ar jama’a.