Yanzu haka dai ‘yan Najeriyar na bayyana mabanbantan ra’ayoyii da kuma matakai akan kamfanonin Afirka ta kudu dake aiki a Najeriya.
A jiya ne dai hukumomin Najeriya suka umarci jakadan kasar a Afrika ta kudu da ya koma gida, Inda su-ma mahukunta a Afrika ta kudun suka janye nasu jakadan a Najeriya.
Hakan dai na nuna, yadda alakar diplomasiyya ke kara tabarbarewa a tsakanin kasashen biyu.
A nasu bangaren, kamfanoni da cibiyoyin hada hadar kasuwanci mallakar kasar Afirka ta kudu a Najeriya kamar Kamfanin Sadarwa na MTN, da kantin Shoprite, na fuskantar kauracewar wasu abokan huldar ‘yan Najeriya.
Koda yake tun a shekaranjiya talata kamfanin MTN ya bada sanarwar rufe ofisoshin sa a sassan Najeriya bayan farmakin da wasu a jihar Legas suka kaiwa ofishini, amma kantin shoprite a Kano ya kasance a bude.
Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5