DandalinVOA Ya Sami Bakuncin Mawaki Ibrahim I S

Ibrahim I S

A shirinmu na nishadi a wannan makon mun sami bakunci Ibrahim I S wanda ya shafe shekaru goma yana wannan sana'a kuma ya ce sha'awa ce ta ja shi ga harkar waka.

Sannu a hankali kamar yadda mawakin ya ce Abubakar Sani ne gwarzon sa a waka, ya kara da cewa lokuta da dama ko bashi ya yi waka ba idan ya fara saurare baya sanin lokacin da yake fara rera wa shima.

Matashin ya ce wakar da aka fi sanin sa da ita itace wakar Ina son ki Malama, wadda ya bayyana cewar yayi wakar ne a misalin tamkar dalibin da ke kaunar malamar sa.

Daga karshe ya ce babban burin sa a harkar waka ita ce yaga masana'antar su ta sami tsabtacewa kamar yadda ya kamata, kuma yana bukatar ganin mawaka sun kara hada kawunan su a duk inda suke domin samun ci gaba.