Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Hana Saka Kayan Turawa Don Suna Bata Tarbiyya A Kasar Koriya Ta Arewa


Kasar Koriya ta Arewa “North Korea” ta haramta ma maza ‘yan kasar saka wandon Jeans, da ajiye gashi mai tsawo ga maza, haka mata baza su gyara kai da fuska ba da zasu yayi kama da yadda turawa sukeyi. A cikin wannan yunkurin sunyi nuni da cewar hakan shine kawai hanyar da zasu bi don kare al’adun su. Sun ayyanar da wannan dabi’ar a matsayin hanyar bata yara da al’uma, bayaga bacewar al’adun su.

Sun lura cewar al’adun kasashen turawa na neman boye nasu al’adun na gargajiya. Hakan yasa suka saka wannan dokar, da cewar duk wanda aka samu da saka wando da aka dinkan shi daga yadin Jeans, ko ya bar gashin kanshi ya wuce inci 3, ko kuma aka samu mace tayi kwalliya irin ta turawa to zasu fuskanci fushin hukuma.

Tun a shekarar 2004 ne, kasar ta fara yaki da al’adun kasashen turawa, wanda suka umurci matasa da su yanke gashin kansu, su barshi dai-dai da na ‘yan gwagwarmaya. Shugaban kasar dai Kim Jong-un, yana yaki da duk wani abu da yayi kama da rayuwar turawa. A wani sabon lale da aka dauki matasa aiki don yawo a kan tituna, suna duba matasa maza da mata da suka sa kaya irin na turawa, da takalmi, gyaran gashi. Haka hakkin matasan ne su gano ‘yan mata da basu da aure suke sana’a a kasuwani don hukunta su.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG