Volodymyr Zelenskiy, dan shekaru 41 da haihuwa, wanda jarumin dan wasan barkwanci ne mai fitowa a shirin talabijin, ya lashe zaben shugagaban kasar Ukraine da gagarumin rinjaye wanda aka yi jiya Lahadi, bayan da aka kammala kada kuri’ar, sakamakon jin bayanan masu kada kuri'a ya nuna ya samu kashi 73 cikin 100 na kuri’un a zagaye na karshe da aka yi – wanda ya kusan ninka na abokin hamayyar, shugaba mai ci Petro Poroshenko, har sau uku.
Zelenskiy ya fada wa taron magoya bayansa, yayin da suke murna a Kyiv jiya Lahadi, cewa, “Wannan nasarar tamu ce gaba daya. Ina godiya ga ko wannenku, yanzu babu wasu jawabai da zan yi muku, ina so nace, na gode."
Yayin da yake amsa shan kaye a jiya da daddare, Poroshenko ya mika sakon taya murnarsa ga Zelenskiy, sannan ya kuma kara da cewa, “zan bar ofishina, amma ina so na sanar da tabbacin, ba zan bar fagen siyasa ba."
Daga baya Poroshenko ya rubuta wani sako a Twitter cewa, “Da gani ka san ana cike da murna a Fadar Shugaban Rasha ta Kremlin kan wannan zaben. Su na ganin tunda an samu sabon Shugaba wanda bai da gogewa, kasar Ukraine za ta gaggauta komawa kan falakin da Rasha za ta rika jujjuya ta.