Dan Wasan Barkwanci Basketmouth Da Matarsa Elsie Sun Rabu

Basketmouth da matarsa Elsie (Hoto: Instagram/Elsie Okpocha)

A farkon makon nan wata babbar kotun tarayya a Abuja, ta raba auren Paul Okoye (Rude Boy) na kungiyar mawakan P - Sqaure da matarsa Anita bayan rashin jituwa da suka samu a wani rikici da ya faro tun a bara.

Dan wasan barkwanci nBright Okpocha, wanda aka fi sani da Basketmouth da matarsa Elsie a Najeriya sun rabu.

Basketmouth ne ya sanar da rabuwar tasu a shafinsa na Instagram a ranar Alhamis.

“Duk da ina mai bakin cikin kwarmata al’amuran rayuwata a baina jama’a, wannan wani al’amari ne da ba za a iya kaucea masa ba.

“Bayan tattaunawa mai zurfi da muka yi, ni da matata, mun yanke shawarar mu kawo karshen aurenmu.” Basketmouth ya ce.

A shekarar 2010 Basketmouth da Elsie suka yi aure, suna da yara uku.

“Duk da cewa, kowa zai kama hanyarsa, za mu ci gaba da aiki tare wajen kulawa da ‘ya’yanmu.”

A farkon makon nan wata babbar kotun tarayya a Abuja, ta raba auren Paul Okoye (Rude Boy) na kungiyar mawakan P - Sqaure da matarsa Anita bayan rashin jituwa da suka samu a wani rikici da ya faro tun a bara.

A watan Yunin bana kuma, jaruma Funke Akindele da mijinta Abdulrasheed Bello, wanda aka fi sani da JJC Skillz su ma suka rabu.